Resumen del episodio
Shirin 'Al'adunmu Na Gado' zai duba yadda mahukunta a jihar Bauchi suka dakatar da Mai Martaba Sarkin Lame. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar, Mai Martaba Alhaji Aliyu Yakubu Lame, daga jagorantar harkokin masarautar bisa zargin aikata ba daidai ba. Gwamnan ya kuma amince da kafa kwamitin mai mambobi 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken, inda aka ba kwamitin wa’adin makonni uku domin gabatar da rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati. Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama, da kuma rahotannin sirri daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro kan zargin amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, yin amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba da sauran halaye da ake ganin sun saɓa da nauyin da ke kan mai sarautar gargajiya.

Episodios
Yadda gwamnan Bauchi ya dakatar da Mai Martaba Sarkin Lame
EscuchadoShirin 'Al'adunmu Na Gado' zai duba yadda mahukunta a jihar Bauchi suka dakatar da Mai Martaba Sarkin Lame. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar, Mai Martaba Alhaji Aliyu Yakubu Lame, daga jagorantar harkokin masarautar bisa zargin aikata ba daidai ba. Gwamnan ya kuma amince da kafa kwamitin mai mambobi 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken, inda aka ba kwamitin wa’adin makonni uku domin gabatar da rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati. Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama, da kuma rahotannin sirri daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro kan zargin amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, yin amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba da sauran halaye da ake ganin sun saɓa da nauyin da ke kan mai sarautar gargajiya.
Yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa a ƙasar Togo
EscuchadoShirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa ya sake leƙawa ƙasar Togo a wannan mako, inda ya duba yadda Hausawa ke gudanar da sana'ar Fawa.
Mahukunta na yunkurun sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Nijar
EscuchadoShirin Al'adun Mu Na Gado na wannan mako yayi duba ne kan yunƙurin sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Niger da magabatan ƙasar suka dauri aniyar yi. Tun bayan juyyin milki da sojojin ƙasar Niger suka yi da niyar raba gari da suka yi da duk wani gadon Turawan mulkin mallaka da suka mullaki ƙasar, sun ga dacewar sake rubuta tarihin ƙasar domin galibinshi tarihi ne da Turawan suka rubuta abinda yayi musu, wanda wani lokacin ma ba gaskiya bane ko kuma an masa gyaran fuska. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa...............
Yadda al'ummar Hausawa kusan dubu 30 ke rayuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar Togo
EscuchadoShirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya tsakanin su ba tareda an fuskanci wata matsala. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdoulaye Issa................
Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar
Escuchado'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.