Resumen del episodio
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Episodios
Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu
EscuchadoShirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar
EscuchadoShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dama ta samu. Ku latsa alamar sauto don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta Ingila
EscuchadoShirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda al’amura ke gudana a gasar Firimiya lig ta Ingila. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa
EscuchadoShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi. Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Shugabanni hukumar NFF sun yi murabus bayan kiraye-kirayen ƴan Najeriya
EscuchadoShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa. A cewar rahotanni, 8 daga cikin mambobin kwamitin 13 ne suka yi murabus daga jagorancin hukumar ta NFF, lamarin da ya haifar da shakku gameda zaɓen shugabannin hukumar da za a yi nan ba da jimaba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............